Jaridar Akhbar da ake bugawa a Lebanon ta nakalto wata majiya mai tushe dake cewa kasar Masar ta ki yarda da shawarar Saudiyya na aikewa da sojoji zuwa cikin Yeman domin yaki da Ansarullah.
Majiyar ta ce, Masar ta Fifita bayar da hankali akan kare hanyoyin sufuri na ruwa da kuma bayar da fifiko akan nemo hanyoyin siyasa na warware matsalar Yemen.
Tattaunawar da aka yi a tsakanin jami’an Saudiyya da Masar ta mayar da hankali ne akan kare tattalin arzikin kasar Saudiyya da kaucewa fadawa yin fada kai tsaye da kungiyar Ansarullah da kawayensu na wannan yankin.
Masar ta yi alakawalin bayar da kariya ga hanyoyin kasuwanci da zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci da kawar da duk wani hatsari da za su fuskanta.
Jaridar ta Akhbar ta kuma ce; Masar ba ta karbi shawarar Saudiyya ba na aikewa da sojojin kasa cikin Yemen, wanda ba a san yadda za ta kare ba,saboda yanayin kasar Yemen mai sarkakiya.
Yarima mai jiran Gado ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Masar kwanaki kadan da su ka gabata, inda ya tattauna halin da ake ciki a wannan yankin da kuma fadan dake faruwa a tsakanin kasarsa da Yemen.
Saudiyya da gwamnatin da take goyawa baya a birnin Aden sun kai hare-hare a filin saukar jiragen sama na Sanaa, da shi ne ya yi musabbabin dawowar yaki.
Yan zuwa yanzu dai Ansarullah sun kwace iko da dukkanin garuruwa da tsibirun da suke zagaye da Babal-Mandab da hakan ya ba su Karin shimfida iko akan yankuna mafi girma na Yemen.