Wadanda Su Ka Yi Garkuwa Da Malaman Addini A Jahar Zamfara Sun Nemi Kudin Fansa

Wadanda Su Ka Yi Garkuwa Da Malaman Addini A Jahar Zamfara Sun Nemi Kudin Fansa
jahar zamfara

Jaridar “Daily Trust” na Nigeria ta buga labarin dake cewa, wadanda su ka yi garkuwa da malaman addini shida a Jahar Zamfara sun bukaci a ba su Naira miliyan 30 kafin su sake su.

 Jaridar ta ambato wata majiya a kauyen Dakko dake karamar hukumar Bakura ta bakin malam Muhammad Ibrahim yana tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Malam Ibrahim ya kuma fada wa jaridar cewa, tuni an saki matukin motar dake dauke da malaman da aka sace, bayan da aka biya Naira miliyan 2.

Haka nan kuma ya ce, yawan mutanen da masu garkuwa da mutanen su ka sace takwas ne, biyar daga cikinsu limamai da matukin motarsu, sai kuma wasu mutane biyu da suke kan hanyarsu ta zuwa gona.

Bugu da kari ya ce, sun sami labarin yadda masu garkuwa da mutanen su ka bukaci a ba su Naira 300,000 akan kowane mutum daya daga cikin mutane biyu manoma, da kuma fetur lita 25. Amma akan matukin limaman, mutanen sun bukaci Naira miliyan 2 ne daga iyalansa.

Tuni an saki matukin a jiya Asabr kuma tuni ya koma cikin iyalansa a kauyen Kwatsama. Haka nan kuma yanzu ana Shirin biyan Naira miliyan 30 domin sakin limaman.

Wata majiya mai kwari ta ce wani dan majalisar dattijai ne daga Jahar ta Zamfara ya yi alkawalin biyan kudaden. Malaman da aka sace dai su ne;

Malam Muhammadu Shehu limamin juma’a na Dakko, sai malam Murtala Dakko da shi ne na’ibin liman. Sai kuma malam Muhammad Yahuza da shi ne da shi ne limanin Dogon madaci. Malam Magawata Abdullahi, sai Bala Hogun da Malam Muhammad Tasi’u. Dukkaninsu limaman juma’a ne a dogon Madaci da kwatsama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted