Tuhumar Mutane 159 Dangane Da Kashe Jagora Ali Khaminaei(q)

Kakakin ma’aikatar shari’a a nan Tehran ya bada sanarwan cewa an gabatar da sunayen mutane 159 tsakanin Amurkawa da kuma yahudawan HKI dangane da kashe

Kakakin ma’aikatar shari’a a nan Tehran ya bada sanarwan cewa an gabatar da sunayen mutane 159 tsakanin Amurkawa da kuma yahudawan HKI dangane da kashe jagoran juyin juya halin musulinci Imam Sayyid Alitul Khamaniaei(q) da wadanda aka kashesu tare da shi a gaban kotu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Ali Kazemi kakakin ma’aikatar shari’a yana fadar haka ya kuma kara da cewa, mutanen sun hada da manya manyan Jami’an gwamnatin Amurka yan siyasa da sojoji. Har’ila yau da kuma irinsu a hKI. Yace Amurkawa 92 sannan yahudawa 67, kuma tuni an gabatar da karar a gaban kotu.

Kazemi ya kara da cewa masu shigar da kara a wannan shari’ar suna neman dukiya da nadama da diyyar wadanda aka kashe. Kotun da aka gabatarwa karar ta bayyana cewa zata saurari shari’ar har zuwa yanke hukunci sannan za’a bayyana lokacin fara sauraronta nan gaba.

Dangane da kwamandojojin sojojin da suka yi shahada kuma, kakakin ma’aikatar shari’ar y ace an tsara kararraki har 15 inda anan ma ake tuhumar Amurkawa 97 da kuma yahudawan Sahyoniyya 23. Banda haka Kazimi ya bayyana cewa ana kan kammala wata karar kan kissan Dr Shahid Ali Larijani, (Sakataren majalisar koli ta tsaron kasa) da Mustafa Larijani wato dansa, da kuma wani da ke tare da su. Daga karshe yace manufar dukkan wannan shi ne ci gaba da sauraron karar a cikin gida ko a kotunan kasa da kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted