Rundunar tsaro ta farar hula ta kasa ( NSCDC) ta aike Abdulhamid Salisu Kabara a matsayin sabon kwamanda zuwa Jahar Niger.
A wata sanarwa da shugaban ofishin hulda da jama’a na rundunar tsaro ta farar hula Abubakar Rabiu Muti ya fitar, ya bayyana cewa; Kabara ya karbi shugabancin rundunar daga Suberu Siyaka Aniviye wanda aka dakatar da shi bayan mutuwar masu hako ma’adanai 37 a lokacin da suke a tsare.
Muti ya kuma ce; Kabara ya karbi shugabancin rundunar ce a wani lokaci mai hatsari bayan abin takaicin da ya faru na mutuwar masu hako ma’adanai din da aka kama saboda sabawa doka.
Haka nan kuma ya ce; Kabara ya nuna bakin cikinsa akan rashin da aka yi na rayuka, sannan kuma ya mika sakon juyayi ga iyalan wadanda su ka kwanta dama.
A Jahar ta Niger, jami’an rundunar tsaro ta farar hula sun kama masu hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba, tare da tsare su a dakunan da babu wadatacciyar iska a ciki.
Wadanda su ka tsira daga hannun jami’an tsaron na farin hula, sun bayyana yadda wahalar da su ka sha a lokacin da suke tsare saboda zama cikin kananan dakunan da babu wadatacciyar iska, da ya sa suke lumfashi dakyar.
Wani daga cikin wadanda su ka tsirar ya shaida wa manema labaru cewa; mun rika ihu da kururuwa suna neman taimako, sannan muna fada musu cewa wasu daga cikinmu suna mutuwa, amma ba su yard da abinda muke fada ba.” An tura jami’an tsaro da dama akan titunan birnin Minna domin kwantar da hankali