Ma’aikatar sharia a nan Iran ta zartar da hukuncin kisa kan wani dan leken asirin HKI wanda ya dade yana aiki da hukumar Sosad na HKI. Wanda kuma sanadiyyar sakonnin da ya aikawa hukumar da dama daga cikin Jami’an tsaron JMI sun kai ga shahada.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar shari’ar tana cewa Hussain Pedaran ya aikawa hukumar Mosad ta HKI asiran sojojin JMI a birnin Esfahan, daga ciki har da wuraren da aka boye makamai.
Wannan ya faru a yakin kwanaki 12 wato a cikin watan Yulin shekara ta 2025 da kuma yakin da ake ciki.
Sannan banda sakonnin da Jami’an tsaro suka gano a kan wayarsa da kayakin lantarkinsa, shi da kansa ya tabbatar da cewa ya dade yana aiki da Mosad, banda haka shi ne ya fara neman ita MOSAD da kuma CIA don yayi masu aiki.
A cikin sakonnin da ya aikata masu har da sunaye da adireshi da kuma hatta lambobin wayar wasu jami’an sojojin kasar Iran , da inda gidaje da wurare aikinsu suke, kuma daga baya sun yi amfani da bayanan da suka bashi suka kuma kashe wadannan jami’an sojoji.