Gwamnatin kasar Siriya karkashin shugabancin kungiyar HTSH ta ki amsa kiran gwamnatin kasar Saudiya na taimaka mata a yakin da take fafatawa da kungiyar Ansarallah na kasar Yemen.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shafin labarai na jaridar Turkey Today tana fadar haka ta kuma kara da cewa sojojin kasar Yemen sun sami nasarori masu yawa kan mayakan saudiya a kudancin kasar ta Yemen.
Daga cikin nasarorin sojojin Yemen sun kakkabo jirgin yakin kasar Saudiya samfurin F 15 . Sannan ta maida ikon gwmnatin Yemen kan yankuna masu muhimmanci a mashigar ruwa ta babaul mandab.
Kafin neman sojojin HTS dai kasar Saudiya ta nemi irin wannan taimakon daga kasashen yankin da kasashen yamma da dama, ba tare da wani ya amsa daga wajensu ba.
Ansarullah dai tana bukatar Saudia ta kawo karshen takunkuman tattalin arzikin da ta dora mata kimani shekaru 12 da suka gabata.