A wata ziyarar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya kai garin Lamerd na lardin Fars a kudancin kasar Iran a cikin yan kwanakin da suka gabata, ya bayyana cewa Amurka ta yi amfani da makaman da aka haramta a fagen kasa da kasa a hare haren da ta kaiwa zauren wasanni a garin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Baghaei yana fadar cewa, Amurka ta yi amfani da makaman guba a cikin boma boman da ta jefa a zauren wasanni na garin Lamerd wanda ya kai ga mutuwar mutane akalla 22. Ya ce, Amurka ta yi amfani da makamai mai linzami masu kananan boma boma har 180,000 wadanda suka tarwatse suka wasu a ciki da wajen zauren wasanni.
Ya ce: Kananan boma bomai da suka tarwatse sun yayyaga jikin shahidi mafi karancin shekaru da makamin ya kashe wato Ayina yar shekaru 2 a duniya.
Baghaei ya ce, tare da binciken da ma’aikatar kiwon lafiya ta gudanar ta gano cewa boma baman da Amurka ta jefa kan zauren wasanni na Larmerd suna dauki da wani sinadari wanda saurin kashewa don yawaida wadanda zasu mutu.
Yace makamai masu linzami hudu ne dauke da dubban kananan boma bomai suka fada a wurin a cikin second 35 kacal.
Sannan bayan haka ne ta jefa makamai masu linzami na tomahok kan makarantan firymari a Minab.