Iran Da Pakistan Sun Tattauna Dangane Da Matsalolin Yankin Asiya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Pakistan Ishaq Dar inda suka tattauna dangane da makamashi

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Pakistan Ishaq Dar inda suka tattauna dangane da makamashi da kuma yanda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz ta yi tasiri a harkokin kasuwanci a duniya.

Tashar talabijan ta Presstv ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan na cewa jami’an gwamnatocin biyu sun yi magana dangane da yanda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz ta shafi harkokin kasuwanci a duniya.

Sai kuma kakakin ministan cikin gida na kasar Iran Ali Zainiyand ya ce, a halin yanzu ana ci gaba da tattaunawa dangane da yanda za’a dawo kan teburun tattaunawa bisa sharuddan Iran. Sharudda wadanda JMI ta amince da su, daga ciki har da jagoran Juyin juya halin musulunci Aya. Mojtaba Khaminaei. Kuma shi ne fahintar juna na Islamabad.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted