UNICEF: Gaza Ta Zama Wajen Mutuwar Yara Kanana A Duniya

Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa zirin Gaza a kasar Falasdinu da aka mamaye ya zama wurin mutuwa ga

Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa zirin Gaza a kasar Falasdinu da aka mamaye ya zama wurin mutuwa ga yara. Ta kuma bukaci a dauki matakan gaggawa don ganin an kaicewa mutuwar gama gari saboda yunwa a yankin.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Jems Addar wani jami’in hukumar UNESCO yana fadar haka a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta IBC ya kuma kara da cewa. Yara kanana a Gaza, a dai dai lokacinda suke barci boma boman jiragen yakin HKI suna iya faduwa a kan gidajensu ya kuma kashe su a ko wani lokaci.

Jami’in yay i kira da HKI kan cewa dole ne ta yi aiki da wajibinta na bude dukkan kofofin shigar da kayakin agaji a cikin Gaza, saboda ceton rayuwan mutanen yankin musamman yara kanana daga karancin abinci mai gina jiki da kuma yunwa wanda ya fara bayyana a yankin.

Jims ya kara da cewa tsagaita wuta ya zama wajibi, saboda jami’an agaji ba zasu iya shiga cikin yanki a dai dai lokacinda ake ruwan wuta a kan mutanen gaza ba.

Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda HKI ta ki amincewa da nisihar da kawayenta suka bata dangane da rayuwar  mata da yara a gaza , da kuma sauran kasashen duniya suka bata na dakatar da wuta. Sannan abin damuwa shi ne taki ta yi aiki da hatta kuduririn MDD da kuma na kotun kasa da kasa dangane da yaki a Gaza.

Tun cikin watan Octoban da ya gabata ne HKI ta fara luguden wuta ta sama da kasa da ruwa kan mutanen gaza inda ya zuwa yanzu ta kashe mutane kimani 33 a yankin mafi yawansu mata da yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments