TUC : Karin Albashi Ma’aikatan Najeriya Ke Bukata Ba Tallafi Ba

kungiyar TUC tace kungiyar TUC karin albashi maaikatan nijeriya ke so ba tallafin kudin mota na dubu 70ba

Ƙungiyar kwadago ta TUC a Najeriya ta yi watsi da tayin gwamnatin Tarayya na fara biyan naira dubu 70 ga ma’aikatan kasar a matsayin tallafin sufuri, wanda za a shafe watanni 6 ana yi, inda kungiyar ta bukaci karin albashi cikin gaggawa ga dukkan  ma’aikatan maimakon tallafin mai na kayyadadden lokaci.

A ranar talata ne aka cimma matsaya tsakanin gwamnatin Najeriyar da NLC da kuma hadakar kungiyoyin kwadago a taron da ba a ga wakilcin TUC a ciki ba, sai dai a sanarwar da ta fitar  a jiya Laraba kungiyar ta ce tallafin na matsakaicin lokaci bai wadatar ba kuma ba zai  magance matsalolin da aka jefa ma’aikata a ciki ba.

TUC ta kuma zargi gwamnatin Najeriya da kasa cika alkawarinta na 2023 game da gyaran albashin ma’aikata baya ga watsi da yarjejeniyar watanni ta gyare-gyare ga tsarin albashin ma’aikatan bangaren lafiya.

Wasikar ta TUC ta ce, gwamnatin ba ta da bukatar doguwar tattaunawa da bangarorin game da mafi karancin albashi kafin aiwatar da karin albashin a halin da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted