Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kofar tattaunwa da kuma diblomasiyya a bude take tsakaninta da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, idan ta ga dama ta tuntube be mu da hanyar, wannan a yayinda hannayemmu suna kan kunamun wutan makamammu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a shafinsa na yanar gizo wato X, a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa Iran zata ci gaba da tuntubar masu shiga tsakaninta da Amurka a ko yauce, don sauraron jin , labarin amincewa da sharuddanta guda 7 wadanda ta shimfida wa Amurka saboda bude mashigar ruwa ta Hurmuz.
Wannan a dayan bangaren kuma a shirye take ta kare kasar daga duk wani kokarin mamayar kasar ko kwace mashigar ruwa ta hurmuz daga hannun makiya.
Dakarun IRGC na Iran sun sami nasarar rufe mashigar ruwa ta Hurmuz ne bayan da Amurka ta farwa kasar da yaki a ranar 28 ga watan Fabrayru na shekara ta 2026. inda ta hana jiragen ruwa dauke da man fetur shiga ko fita zuwa kasashen larabwa na yankin sai tare da sharuddanta. Banda haka tana samun goyon bayan mutanen kasar.