Falastinu: An Saki Farh Abu Ayyash Bayan Kwanaki 450 A Tsare

Farh Ayyash yar jirida wacce take aikowa kamfanin dillancin labaran tasnim labarai daga garin Khalil na yankin yamma da kogin Jordan ta sami yencinta a

Farh Ayyash yar jirida wacce take aikowa kamfanin dillancin labaran tasnim labarai daga garin Khalil na yankin yamma da kogin Jordan ta sami yencinta a yau Alhamis, bayan da ta share fiye da shekaru biyu da rabi tsare a hannun sojojin yahudawan sahyoniyya.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya bayyana vewa a ranar 6 ga watan Augustan shekara ta 2025 ne sojojin yahudawan suka kutsa cikin gidanta a garin Bait Amr kusa da garin Khalil na yankin yamma da kogin Jordan a cikin dare, suka kamata suka tsare.

Labarin ya kara da cewa, gwamnatin yahudawan sun tsare ta karkashin wata doka da suke kira dokokin gudanarwa, inda suka tsareta ba tare da gabatar da ita a gaban kotu ba na wani lokaci . sannan bayan sun gabatar da ita kuma sai suka yi ta shishigi a cikin shari’arta har zuwa wannan lokacin.

Gwamnatin yahudawan tana zarginta da yada labaran da basa so ga wadanda take masu aiki.

Daga karshe, alkalin wata kotun yahudawan ya wanke ta daga aikata wani alifi a jiya wanda ya bada damar sakinta bayan kimani shekaru 2.5 ko kwanaki 450.

Farh Abu Ayyash ta tabbatar da cewa yahudawan sun azabtar da ita a lokacinda take tsare a hannunsu a wannan lokacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted