Kafafen yada labaran JMI sun Bada labarin asar wasikar neman tattaunawa da JMI wanda mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance ya aikawa sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iram Mohsen Rezaei.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar jami’an tsaron kasar Iran na fadar haka a jiya Alhamis, amma zasu yi nazarin wasikar su kuma kuma bada amsarta a lokacinda ya dace.
Wasikar, kamar yanda wasu suka bayyana bata bayyana yanda tattaunawar zata kasashen ba, amma bata ambaci bukatar Iran na cika sharuddanta guda 7 kafin bude mashigar ruwa ta Hurmuz ba. A ranar 28 ga watan Fabrayru na wannan shekarar ne sojojin Amurka da HKI suka farwa kasar Iran da yaki da nufin kifar da gwamnatin kasar da kuma mamayeta. Kuma sun kashe jagoran juyin juyahalin musuluncin kasar a ranar ta farko na fara yakin. Sun kuma kashe manya manya Jami’an tsaro wadanda suka hada da ministan tsaro da kuma manya manyan kwamandojin sojojin kasar. Amma maida martanin sojojin kasar da kuma goyon bayan da mafi yawan mutanen kasar suke bawa gwamnatin JMI ya rikita al-amura ga Amurka da HKI. Bugu da kare , sojojin Iran sun sami nasarar rufe mashigar ruwa ta Hurmuz a farkon yankin.