MDD Ta yi Tir Da Takunkumin Da Aka Sanyawa Kasar Cuba

majalisar dinkin duniya ta yi tir da takunkumin da aka kakabawa kasar kuba duk da kokarin diflomasiya da amurka tayi na kara amincewa da kudurin

Majalisar dinkin duniya ta kada kuri’a a karo na 34 don neman amincewa da wani kuduri dake Allah wadai da takunkumin tattalin arziki da amurka ta kakabawa kasar Cuba, duk da kokarin diflomasiya da Washington tayi na adawa da wannan kuduri da ake gabatarwa a duk shekara

An gabatar da kudurin ne a jiya laraba inda aka kada kuri’u 130 ta amincewa da kudurin sai kuma 17 ta nuna rashin amincewa yayin da guda 25 kuma suka kauracema kada kuri’ar

A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X shugaban kasar cuba ya bayyana samun goyon bayan mai yawa ga kudurin a matsayin gagarumar nasara ga alummar cuba jarumai,  wadanda basu mika wuya ba ga duk wani matsin lambar tattalin arziki da barazana da cin zarafi daga gwamantin amurka

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted