Wasu Tankokin Mai Guda 3 Sun Tarwatse A Mashigar Hormuz

wasu tankokin maiguda 3 sun fashe bayan sun bi hanyar da aka hana bi ba da izini ba a hormuz

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare juyin musulunci na iran sun sanar cewa wasu tankokin mai guda 3 sun fashe inda suka kama da wuta bayan da suka bi wata hanya ba da izini ba a kudancin Hurmuz bayan da suka ci karo da nakiyoyi

A cikin wani rahoto da aka fitar a ranar Alhamis ofishin dake kula da hulda da  jama’a na dakarun kare juyin musulunci na kasar iran yace jiragen dakon man sun kashe dukkan nau’rorinsu na rada da na jagorantar tafiya, kuma suna kokarin fita ta wata hanya da ba a bada izinin amfanin da ita ba a kudancin Hormuz kuma suka yi watsi da gargadin da rundunar ruwa ta IRIGC ta yi  musu, inda suka kaci karo da nakiyoyin ruwa, lamarin da yasa jiragen man suka fashe.

Rundunar sojin ruwan ta IRIGC ta yi gargadin cewa an sanya nakiyoyi a hanyoyin da baa bada iznin amfani da su ba a cikin mashigun tekuna, kuma masu jiragen ruwa da ma’akatan jirgin su ke da alhakin amfani da wadannan hanyoyin

Ana sa bangaren kakakin dakarun kare juyin musulunci na iran brgedier janaral Hussein Mohebbi ya bukaci rundunar Centcom mai kisan yara kanana da ta tabbatar da ikirarin da tayi na gudanar da ayyukan cire nakiyoyi a Mashigar hormuz, ta hanyar gabatar da hujjojin da zaa iya tantancewa daga bangare mai zaman kansa ba wai ta hanyar bayar da sanarwa kawai ba

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted