Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdulmalik alhuthi ya zargi kasar Amurka da Isra’ila da kuma kasar Birtaniya da hannu wajen hare haren da ake kai mata kuma ya jaddada matsayinsu game da ci gaba da kare alummarsu da kuma batun alummar falasdinu da ake zalunta
A cikin bayani da yayi da aka watsa ta gidajen talabijin din kasar kan zagayowar ranar shahidai sayyid Abdulmalik badarud den al-huthi yace kasar amurka da isra’ila suna ikirarin yanci da samar da yalwar tattalin arziki da kare hakkin bil adama don kare taasar da suke tafkawa , amma haka na kara nuna irin girman zalinci da taadanci da wuce guna da iri da suke yi ne.
Yace amurka ta samu saudiya a wani bangaren larabawa da na musulmi dake aiwatar da hare-haren da kuma daukar nauyinsu, yana zargin gwamnatin saudiya da yin aiki bisa manufofi da tsare tsaren amurka da kasashen yamma, da kuma amfani da taken siyasa don jawo hankalin jama’a ta hanyar dake kara zurfafa rarrabuwar kawuna.