Shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan ya bayyana cewa kasar iran tana aiki tukuru wajen ganin an aiwatar da umarnin jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah sayyed mojtaba Khamenei na ganin an cika sharuddan da Tehran ta gabatar na kawo karshen yakin Amurka da isra’ila suka kakaba mata, da kawo karshen yanayin ba yaki ba zaman lafiya
A lokacin ganawarsa da major ganaral Mohsen Reza’I sakataren majalisar koli ta tsaron kasa jagoran yayi da a kara kaimi wajen ganin an kare hakki da manufofin alummar iran, da yan gwagwarmaya wajen cika sharuddan da jami’an kasar suka sanar na kawo karshen yanayin ba yaki ba zaman lafiya da ake ciki.
A lokacin taron da yayi da mukarraban gwamnati shugaban kasar yayi kira ga dukkan hukumomi da su kasance cikin shiri domin daukar matakai daidai da yadda yanayin yake sauyawa,