Majiyar dakarun IRGC Navy na kasar Iran ta bada Labarin Sauke wani jirgin leken asirin Amurka a sararin samaniyar lardin Humuz a jiya Alhamis, kuma sun sauko da shi kasa ba tare da ya lalace ba.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar na cewa Jirgin leken asirin samfurin MQM-170 na lekenn asiri ne, kuma bayan an kwace sarrafashi daga hannun Amurka aka kuma sauko da shi kasa ba tare da ya lalace ba, sun fahinci cewa ya taso ne daga daya daga cikin kasashen larabawa na yankin tekun farisa ne.
Har’ila yau sun gano cewa umurnin da aka bashi shi ne gani cibiyoyin tsaro na JMI da ke yankin Hurmuz ya aika masu. Don su yi amfani da su nan gaba wajen kawo hare hare kan yankin.
Har’ila yau IRGC Sun Kakkabo Wani jirgin leken asiri samfurin MQ-1 Drone shi ma na Amurka A Hurmuz
Jami’an hulda da jama’a na rundunar ya bada sanarwan cewa, a cikin sa’o’in da suka gabata sun sami nasarar kakkabo wani jirgin leken asiri kuma mai kai hare hare samfurin MQ-1 na Amurka a sararin samaniyar mashigar ruwa ta Hurmuz, kusa da tsibirin Sirik cikin ruwan tekun farisa.
Labarin ya kara da cewa dakarun IRGC masu kula da tsaron sararin samaniya na kasar Iran ne , tare da amfani da tsarin bai daya na kare sararin samaniyar kasar suka gano jirgin suka kuma kakkabo shi a jiya Alhamis. A halin yanzu an kakkabo kimani jirage 54 irin wannan nauin na Amurka tun bayan fara yaki.