Takht Ravanji: Iran Ba Za Ta Taba Yin Tattaunawa Akan Dakatar Da Tace Sanadarin Uranium Ba

Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a

Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami.

Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium da kuma makamai masu linzami, jan layi ne da jamhuriyar musulunci ta Iran ba za ta bari a ketara su ba ba kuma za ta bari a bude tattaunawa akansu ba.

Kwamitin da yake kula da tsaron kasa da kuma siyasar waje a majalisar shawarar musulunci ta Iran a karkashin jagorancin dan majalisar Ibrahim Ridhazi ya yi taro a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka gayyaci mataimakin ministan harkokin wajen domin jin ta bakinsa akan abubuwan da suke faruwa a tattaunawar da ake yi ba kai tsaye ba da Amurka.

Ridha’i ya fada wa ‘yan jarida cewa Takht Ravanji  ya kammadar da rahoto akan yadda tattaunawar take gudana a tsakanin Amurka da Iran da kasar Oman take shiga Tsakani.

Haka nan kuma ya ce; Tace sanadarin Uranium a cikin gida wani jan layi ne da ba za a tsallake shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments