Syria: An Kashe Malami Mai Huduba A Hubbaren Sayyida Zainab ( a.s) Dake Birnin Damascuss

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Syria ta sanar da cewa; ta bude bincike akan yunkurin hargitsa zaman lafiya a cikin kasar. Sanarwar ta kara da cewa;

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Syria ta sanar da cewa; ta bude bincike akan yunkurin hargitsa zaman lafiya a cikin kasar.

Sanarwar ta kara da cewa; kisan gillar da aka yi wa malami mai huduba a hubbaren Sayyida Zainab ( a.s) Sayyid Farhan Hassan Mansur, yana a karkashin hargitsa zaman lafiya a kasar, tare da bayyana abinda ya faru da cewa yana da hatsari mai girma.

Bugu da kari ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Syria ta ce, wannan laifin da aka tafka, ba zai wuce, ba tare da hukunta wadanda su ka aikata shi ba, don haka tuni an fara aiwatar da bincike domin gano ko su waye su ka aiwatar da shi da wanda ya ingiza su, saboda daukar matakai na doka akansu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted