Somaliya ta soki ziyarar ministan harkokin wajen Isra’ila a Somaliland

Somaliya ta yi Allah wadai da ziyarar da ministan harkokin wajen Isra’ila ya kai zuwa yankin Somaliland, wanda ta ce ya shiga yankin ba tare

Somaliya ta yi Allah wadai da ziyarar da ministan harkokin wajen Isra’ila ya kai zuwa yankin Somaliland, wanda ta ce ya shiga yankin ba tare da Izini ba.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Somaliya ta soki ziyarar tana mai cewa “ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Gideon Saar ya yi ya zama babban keta ikon mallakar Somaliya, huriminta, da hadin kan siyasa, kuma yana wakiltar tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Isra’ila ya tabbatar da amincewa da Isra’ila ga Somaliland a matsayin wanda ya yi daidai da “gaskiya.”

Gideon Saar ya je Somaliland makonni biyu bayan da Isra’ila ta amince da wannan jamhuriya da ta ayyana kanta a matsayin mai cin gashin kanta, wadda Somaliya ke ɗaukarta a matsayin wani ɓangare na ƙasarta.

A ranar 26 ga Disamba, 2025, Isra’ila ta zama ƙasa ta farko da ta amince da Somaliland a matsayin “ƙasar da ke cin gashin kan ta” tun bayan ballewarta daga Somaliya a shekarar 1991.

shugaban Somaliland, Abdirahman Irro Da yake magana da manema labarai, ya yi alƙawarin ziyartar Isra’ila nan ba da jimawa ba bisa gayyatar Fira Minista Benjamin Netanyahu.

Shugaban Somaliya ya zargi gwamnatin Yahudawa da sanya wasu sharudda da dama kan wannan amincewa, ciki har da sake tsugunar da Falasdinawa da kuma kafa sansanin soja, zargin da hukumomin Somaliland suka musanta.

Masu sharhi sun yi imanin cewa kawance da Somaliland yana da matukar amfani ga Isra’ila saboda matsayinta na dabarun mashigin Bab-el-Mandeb, domin fuskantar ‘yan Houthi na Yemen, wadanda suka kai hare-hare da dama kan Isra’ila tun farkon yakin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted