Kwamandan mayakan kas ana rudnunar dakarun kare juyin musulunci ( IRGC) Birgediya Janar Muhammad Karami ya ziyarci yankin gabar ruwan tekun pasha, domin ganin yadda dakarun suke cikin Shirin ko-ta-kwana domin fuskantar makiya.
Birgediya janar Muhammad Karami ya kai Ziyara a sansanin dakarun na IRGC na Madina Munawwarah a kudancin gabar ruwan tekun pasha.
A yayin wannan ziyarar birgediya janar Muhammad Karami ya ganewa idanunsa zama cikin Shirin yaki da fuskantar abokan gaba na rundunar take ciki.
Da yake gabatar da jawabi, janar Karami ya ce, dakarun na IRGC suna ci gaba da bibiyar kai da komowar sojojin bakin haure da su ka shigo wannan yankin, kuma suna ci gaba da gudanar da aikinsu domin dakile barazanar abokan gaba.
Haka nan ya kuma ce; Da yardar Allah madaukakin sarki, al’ummar Iran, da sojojinta za su ci gaba da zama cikin Shirin domin mayar da martani akan duk wani wuce gona da irin na makiya.
Har ila yau ya ce, Ba da jimawa ba za a dauki fansar jinin jagora shahidi da kuma sauran shahidai.