Ghana da Najeriya sun yi tir da kyamar baki a Afirka ta Kudu

Kasashe da dama, ciki har da Ghana, Najeriya, Uganda, da Kenya, sun kwashe 'yan kasashensu da dama.

Kasashen Ghana da Najeriya sun yi kira ga kungiyar Tarayyar Afrika da ta dauki mataki kan kyamar baki a Afrika ta Kudu.

Wannan kiran dai na zuwa ne a yayin da ake fuskantar karuwar tashe-tashen hankulan kyamar baki a Afirka ta Kudu.

Kasashen biyu sun yi Allah wadai da wadannan ayyuka bayan wani taro da ministocin harkokin wajensu suka yi.

Najeriya ta sake janyo hankalin hukumomin Afrika ta kudu da su fadakar da matasan su irin gudunmuwar da Najeriya ta bayar wajen samun yancin kan su.

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shetima wanda ya bukaci kungiyar ECOWAS da ta gabatar da korafi na bai daya ga kungiyar kasashen Afrika ta AU kan lamarin, ya ce dalibai ‘yan Najeriya ne suka dinga sadaukar da kudaden su domin bai wa masu gwagwarmayar neman ;yancin Afrika ta Kudu, amma kuma abin takaici a yau, ‘yan kasar ne ke kai hari suna kasha ‘yan Najeriya da kuma kisan su fice daga kasar.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ba da rahoton cewa an kori ‘yan kasashen waje sama da 53,000 ko kuma an mayar da su gida tun bayan kaddamar da kamfen kin jinin baki a Afrika ta Kudu.

Masu zanga-zanga suna neman a tsaurara matakan tsaro a kan iyakoki da korar mutane da yawa, suna zargin bakin haure da taimakawa wajen haifar da rashin aikin yi, karuwar laifuka, da kuma durkushewar ayyukan gwamnati.

Kasashe da dama, ciki har da Ghana, Najeriya, Uganda, da Kenya, sun kwashe ‘yan kasashensu da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted