Duk Wani Hari Akan cibiyoyin Nukiliya Yana Nufin Fadadar Yaki

Sanarwar ta kunshi cewa; " Amurkawa masu laifi, sun yi barazanar kai wa cibiyoyin Nukiliyar jamhuriyar musulunci ta Iran hari,to idan har makiya su ka
babbar shalkwatar sojojin Iran ta mayar da martani akan Amurka

Babbar cibiyar sojan Iran ta ” Khatamul-Anbiyaa” ta bayyana cewa; Idan Amurka ta kawo wa cibiyar Nukiliyar Iran hari, to hakan yana nufin fadadar yankunan da ake yaki.

Sanarwar ta kunshi cewa; ” Amurkawa masu laifi, sun yi barazanar kai wa cibiyoyin Nukiliyar  jamhuriyar musulunci ta Iran hari,to idan har makiya su ka aiwatar da barazanarsu, za mu dauki hakan a matsayin fadada fagen dagar yaki a cikin wannan yankin.

Haka nan kuma sanarwar ta ci gaba da cewa; sakamakon da zai biyo shi ne dukkanin manufofin Amurka da kuma na abokan kawancenta da suke taimakawa hare-harenta, duk za su zama halartattun wurin kai wa bara daga dakarun sojan jamhuriyar musulunci.”

Wannan gargadin dai ya biyo bayan barazanar da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi ne na cewa; Amurka za ta kawo wa cibiyar Nukiliyar Iran ta ” Khohi-Kalang” a gundumar Ispahan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted