Rundunar Sojin Iran ta rusa sansanonin sojin Amurka guda 3 da kuma tsarin makamai masu linzami na HIMARS na abokan gaba a Kuwait
Rundunar Sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da cewa: A mataki na 19 na Operation Thunderbolt, sansanonin sojojin Amurka na Ahmad al-Jabir da al-Udayri, da kuma sansanin Arifjan da ke Kuwait, sun fuskanci hare-haren mayar da martani a safiyar ranar Talata da jiragen sama marasa matuka ciki.
Saboda martanin da ake mayarwa kan miyagun ayyuka da keta yarjejeniyar Babban Shaidan, rundunar sojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai wasu jerin hare-hare a safiyar ranar Talata, a matsayin daukan fansa kan gine-ginen gudanarwa da kula da sararin samaniyya a sansanin Arifjan, da wurin ajiye jiragen sama masu saukar ungulu a sansanin al-Udayri, da kuma ginin rundunar ‘yan ta’adda da ke sansanin Ahmad al-Jabir da ke Kuwait tare da jiragen sama marasa matuka ciki.
Ana daukan Sansanin Arifjan amatsayin yana daya daga cikin manyan cibiyoyin tura sojojin kasa na Amurka a Kudu maso Yammacin Asiya, kuma sansanin al-Udayri yana dauke da jiragen sama na Amurka kirar Apache, Chinook, da Black Hawk.
Sansanin sojin Ahmad al-Jabir shi ma yana taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa sojojin Amurka a Yammacin Asiya kuma ya kasance babban cibiyar a ayyukan sama da sa ido ga kasar.