Kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka ta kira yi gwamnatin soja ta kasar Guinea-Bissau da ta saki saki dukkanin ‘yan adawar siyasa da ake rike da su ba tare da wani sharadi ba.
Sanarwar da kungiyar ta “ECOWAS” ta fitar a yayin taron shugabannin kasashe mambobi da aka yi a kasar Saliyo,ta kuma ce, sakin ‘yan hamayyar siyasar zai taka rawa wajen ganin kimar matakin mika Mulki ga fararen hula.
Sunan tsohon Fira ministan kasar Domingos simoes Pereira wanda kuma shi ne jagoran ‘yan adawa yana cikin wadanda sanarwar ta Saliyo ta bukaci ganin an sake su ba tare da wani sharadi ba.
Shi dai Pereira an zarge shi ne da hannu a cikin badakalar tattalin arziki da kuma hannu ayunkurin kifar da gwamnati a watan Oktoba na 2026.
Sai dai tsohon Fira ministan ya karyata zargin da aka yi masa.
A shekarar da ta gabata ne dai sojojin kasar ta Guinea-Bissau su ka kifar da gwamnatin shugaba Umaro Sissoco Embalo.
An yi juyin mulkin ne dai kwana daya gabanin hukumar zabe ta sanar da sakamakon karshe na zaben da ak ayi.
Tun da kasar ta sami ‘yanci a 1974 take fama da rikice-rikice da juyin Mulki, ta yadda zababben shugaban kasa daya ne kawai ya iya kammala wa’adinsa na Mulki.