Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya bayar da labarin cewa wasu jiragen ruwa biyu na dakon man fetur mallakin Saudiyya sun koma inda su ka fito bayan da sojojin kasar Yemen su ka gargade su da hana su wucewa ta tekun “Red-Sea”.
Rahoton ya ce, jiragen ruwan na Saudiyya su ne “Xin long Yang” da kuma “Rodos” da suke dauke da makamashi zuwa kasuwannin duniya.
Tashar talabijin din al-mayadeen wai watsa shirye-shiryenta daga Lebanon ta ambaci cewa; Daga lokacin da gwamnatin Sanaa ta sanar da cewa ta kakaba wa Saudiyya takunkumi ta ruwa, jiragen ruwa 6 ne mallakin Saudiyyar su ka koma inda su ka fito.
A shekaran jiya Litinin ne dai kakakin gwamnatin sojan Yemen Janar Yahya Sari ya yi sanarwa da a ciki ya bayyana cewa; An shiga shekaru na 12 da Saudiyya take killace da kasar Yemen, ta kasa, ruwa da kuma sama da hana kai da komawa a cikin filayen saukar jiragen sama da tasoshin ruwa da kai musu hare-hare da hakan yake kara jefa mutanen kasar cikin wahala.
Janar Sari ya ce killace Yemen din da Saudiyya ta yi, ba ya kan wata doka, kuma yana cin karo da ‘yan adamtaka,don haka mutanen Yemen suna da hakkin amfani da dukkanin hanyoyin da suke da su, domin kalubalantar Saudiyya.
Yemen din ta sanar da daukar matakin kakabawa Saudiyyar takunkumi ta ruwa da hana jiragenta na ruwa wucewa ta mashigar ruwan ‘Babal-Mandab.”