Rahotanni daga kasar ta Somaliya sun ce fadan ya barke ne a tsakanin sojojin gwamnatin tarayya da magoya bayan tsohon shugaban kasar Abdulaziz Hassan Muhammad Laftagareen a garin Baidoa.
Wani likita a garin na Baidoa ya fada wa manema labaru cewa; An kai mutane 24 da su ka jikkata zuwa asibiti saboda sun jikkata sanadiyyar fadan, kuma daga cikinsu da akwai farar hula daya da ya rasu.
Ma’aikatar tsaron kasar Somaliya ta bayyana cewa; sojojinsu suna mayar da martani akan harin da mutanen Laftagareen da kuma al-saba su ka kai musu.
Sojojin kasar ta Somaliya suna fada da magoya bayan tsohon shugaban kasar Abdulaziz Hassan Muhammad Laftagareen akan wanda zai shimfida ikonsa akan yankin Kudu maso yammacin kasar.