Janar Wahidi: Jinin Shahidan Kohistak Ba Zai Tafi Haka Siddan Ba

Kwamandan IRGC ya janar Wahidi wanda ya aike da sako akan shahidan Khuhistak ya bayyana cewa; Jininsu ba zai tafi haka siddan ba, za a dauki fansa akan wadanda su ka bayar da umarni da kuma aiwatar da wannan laifin.
Sojojin Ukiraniya Suna Guduwa Daga Wuraren Da Ake Ba Su Horo A Kasar Polland

Majiyar kasar ta Polland ta ce ana bai wa sojojin kasar Ukiraniya horo ne a cikin sansanin kasar a karkashin kulawar kasashen Jamus, Denmark da kuma Norway. Kuma ya zuwa yanzu an yi wa sojojin Ukiraniya 30,000 horon yaki da Rasha a cikin kasar ta Polland.
Sojojin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Wa Yammacin Kogin Jordan Hari

Sojojin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da kai wa garuruwan yankin yammacin kogin Jordan hare-hare da su ka hada al-zubabadah dake kudancin Jenin da Hablah a kudancin Qalqaliyah.
Somaliya: Fada Ya Barke A Tsakanin Sojojin Gwamnati Da Magoya Bayan Tsohon shugaban Kasa Laftagareen

Rahotanni daga kasar ta Somaliya sun ce fadan ya barke ne a tsakanin sojojin gwamnatin tarayya da magoya bayan tsohon shugaban kasar Abdulaziz Hassan Muhammad Laftagareen a garin Baidoa.