Sojojin Ukiraniya  Suna Guduwa Daga Wuraren Da Ake Ba Su Horo A Kasar Polland

Majiyar kasar ta Polland ta ce ana bai wa sojojin kasar Ukiraniya horo ne a cikin sansanin kasar a karkashin kulawar kasashen Jamus, Denmark da
sojojin Ukiraniya

Majiyar kasar ta Polland ta ce ana bai wa sojojin kasar Ukiraniya horo ne a cikin sansanin kasar a karkashin kulawar kasashen Jamus, Denmark da kuma Norway. Kuma ya zuwa yanzu an yi wa sojojin Ukiraniya 30,000 horon yaki da Rasha a cikin kasar ta Polland.

 Sai dai rahotannin sun ce ana samun sojojin na kasar Ukiraniya da suke gudu daga wurin da ake ba su horon.

A halin yanzu a can kasar Ukiraniya an bude shari’ar sojoji masu yawa da suke guduwa daga wuraren bayar da horo da kuma filin daga.

A daya daga cikin batun da ake yin shari’a akansa, da akwai wasu sojoji 50 da aka tura zuwa wurin samun horo,amma wadanda su ka koma gida ba su wuce 35 ba,sauran sun yi baton dabo a cikin kasar Polland.

Kasar ta Ukiraniya tana yaki da kasar Rasha a matsayin mai wakiltar kasashen turai tare da kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted