Sojojin Iran Sun Harbo Jirage 370 Na Abokan Gaba Lokacin Yaki

Jami’in Sojin Iran ya sanar da cewa: Rundunar tsaron sama ta sojojin Iran ta harbo jiragen sama 370 na abokan gaba Mataimakin Kodinetan Rundunar Tsaron

Jami’in Sojin Iran ya sanar da cewa: Rundunar tsaron sama ta sojojin Iran ta harbo jiragen sama 370 na abokan gaba

Mataimakin Kodinetan Rundunar Tsaron Sama ta Sojojin Iran, Birgediya Janar Mohammad Sadiqiyyan ya sanar, dangane da yaƙe-yaƙen da aka yi kwanan nan da kuma hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran cewa: Jiragen saman Iran sun kai hare-hare kan jiragen saman abokan gaba 370. Ya jaddada cewa: Tsarin da aka shirya a cikin gida, hadin kan sojojin, da kuma goyon bayan al’ummar Iran sun tabbatar da tsaro da ikon sararin samaniyar kasar.

Kamfanin dillancin labaran “IRNA” ya ruwaito cewa: Birgediya Janar Sadiqiyyan ya bayyana a cikin wani jawabi da ya gabatar kafin hudubar sallar Juma’a a birnin Shiraz (babban birnin lardin Fars a kudancin Iran) cewa: Sojojin Iran, bisa la’akari da kwarewar da suka samu a lokacin yakin kwanaki 12, sun sami damar tsara yakin da ya barke a ranar 28 ga Fabrairu, wanda hakan ya ba su damar kai hare-hare kan jiragen saman abokan gaba sama da 370.

Mataimakin mai kula da rundunar tsaron sama ta sojojin Iran ya kara da cewa: An harbo jiragen sama da jiragen sama marasa matuka ciki na abokan gaba, wani abu da makiya suka ga ba za a iya misaltawa ba, domin sun yi imanin cewa, ta hanyar hare-haren da suka kai, sun sami nasarar kashe dukkan na’urorin radar tsaron sama na kasar a ranar farko ta yakin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted