Sayyid Khatami: Iran Zata Kalubalanci Yakin Tattalin Arziki Kanta

Limamin da ya jagorancin sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Iran ba za ta taba mika wuya ba; hanyar da za a bi

Limamin da ya jagorancin sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Iran ba za ta taba mika wuya ba; hanyar da za a bi wajen kayar da abokan gaba a yakin tattalin arziki tana cikin jihadi da sadaukarwa

Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran, Ayatollah Ahmad Khatami ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba mika wuya ba, yana mai cewa: Kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya kayar da abokan gaba a yakin tattalin arziki a farkon zamanin Musulunci, haka nan kuma cin galaba kan abokan gaba a wannan yakin mai sarkakiya shi ma yana yiwuwa a wannan zamanin ta hanyar jihadi da sadaukarwa.

Kamfanin dillancin labaran “IRNA” ya nakalto Ayatollah Khatami, yayin da yake magana daga kan mumbarin Masallacin Imam Khomeini da ke birnin Tehran a yau, ya yi magana game da rayuwar Annabi, yana cewa: “Ayoyi da yawa a cikin Alqur’ani sun bayyana hanyar da Annabi (SAW) ya bi wajen fuskantar matsin tattalin arziki. Wannan batu ba sabon abu bane; a’a, matsin tattalin arziki ya kasance tun farkon zamanin Musulunci.”

Ya kara da cewa: “Kafirai suna kashe kudinsu don sanya matsin tattalin arziki da cimma burinsu, amma suna yin nadama da sauri lokacin da suka fahimci gazawar kokarinsu, kuma makomarsu a Lahira za ta kasance azaba da hasara.”

Ya ci gaba da cewa: “Tsarin takunkumin tattalin arziki da Amurka ta sanya yana neman cimma manufofi iri ɗaya, amma kamar yadda aka kayar da maƙiyan Musulunci na farko a yaƙin tattalin arziki, haka nan ma makiyan Musulunci a wannan zamanin za a kayar da su, ko a fagen tattalin arziki ko na soja.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted