Sojojin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da kai wa garuruwan yankin yammacin kogin Jordan hare-hare da su ka hada al-zubabadah dake kudancin Jenin da Hablah a kudancin Qalqaliyah.
Bugu da kari wasu garuruwan da sojojin mamayar su ka kai wa harin sun kunshi Bani Na’im dake gabashin Khalili, da Abu Saninah a kudancin Khalil.
Sojojin na HKI sun kuma kai wa yankin ‘al-fariah’ dake kudancin Tubas hari inda su ka yi taho mu gama da samarin falasdinawa.
Sojojin na mamaya sun kuma kama samarin falasdinawa tare da yin awon gaba da su.
A cikin kwanakin bayan nan dai sojojin Hamramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da kai wa yankin yammacin kogin Jordan hari, a lokaci daya kuma yahudawa ‘yan share wuri zauna suna kai wa gidaje da gonakin Falasdinawa hare-hare tare da kona su.