Janar Wahidi: Jinin Shahidan Kohistak Ba Zai Tafi Haka Siddan Ba

Kwamandan IRGC ya janar Wahidi wanda ya aike da sako akan shahidan Khuhistak ya bayyana cewa; Jininsu ba zai tafi haka siddan ba, za a
janar wahidi

Kwamandan IRGC ya janar Wahidi wanda ya aike da sako akan shahidan Khuhistak  ya bayyana cewa; Jininsu ba zai tafi haka siddan ba, za a dauki fansa akan wadanda su ka bayar da umarni da kuma aiwatar da wannan laifin.

Janar Wahidi ya fitar da skaon yin Allawadai da harin da sojojin Amurka su ka kai a ranar Taalata akan wani bikin aure, a gundunar Hurmuzgan wanda ya yi shahadar mutane da dama da suke halartar bikin aure.

 Janar Wahidi ya bayyana wannan harin da cewa laifi ne na ta’addanci da rashin ‘yan’adamtaka da Amurka ta yi kuma manufarsa ita ce raba mutane da farin cikin da suke ciki da kuma jefa su cikin razana da tsoro da fargaba.

Janar Wahidi ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan shahidaan yana mai jaddada cewa jinin shahidan ba zai tafi haka siddan ba, domin za a dauki fansa akan wadanda su ka bayar da umarnin harin da kuma wadanda su ka aiwatar da shi.

Amurkan dai ta kai hari ne akan gidajen fararen hula a garin Khohistak da ya yi sanadiyyar shahadar mutane 5 da jikkata wasu mutane 70.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted