Araqchi Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Kasar Jordan

Ministan Harkokin Wajen Iran ya mayar wa takwaransa na Jordan martani cewa: Har yaushe Iran za ta jira kafin ta mayar da martani wa mai

Ministan Harkokin Wajen Iran ya mayar wa takwaransa na Jordan martani cewa: Har yaushe Iran za ta jira kafin ta mayar da martani wa mai kai mata hari?!

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani ga kalaman da Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi ya yi kwanan nan.

Araqchi ya rubuta a dandalin X cewa; Don mayar da martani ga kalaman Safadi: “Har yaushe Ministan Harkokin Wajen Jordan zai yi tunanin Iran ya kamata ta jira kafin ta mayar da martani ga mai kai mata hare-haren wuce gona da iri, wanda ba ya girmama ikon mallakar Larabawa ko na Iran?”

Araqchi ya ƙara da cewa: Shin da gaske ne Safadi  bai san cewa an yi amfani da sararin samaniyar kasashen Larabawa, ƙasa, da ruwa wajen kai hare-haren wuce gona da iri na Amurka kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan kasar Iran marasa laifi ba?

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted