Rundunar sojan kasar Yemen ta sanar da kakkabo jirgin sama maras matuki na Saudiyya a karo na uku cikin sa’o’i 24 wanda ya rika shawagi a sararin samaniyar garin al-Baidha’a.
Sanarwar da rundunar sojan na Yemen ta fitar ta kunshi cewa jiragen da ta harbo samfurin ” Wing Loong 11″ da aka yi amfani da makaman da su ka dace wajen kakkabo su.
Sojojin Yemen dai sun gargadi kasar Saudiyya da ta kawo karshen killace Yemen da ta yi, ko kuma ta ci gaba da fuskantar hana jiragen ruwanta na dakon man fetur wucewa ta mashigar Ruwan Babal-Mandab.
Saudiyya ta kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Yemen ne a 2022, sai dai kuma ta keta ta a cikin watan Yuli da ya gabata.