Iran Ta Ce Amurka Ce Ta Fara Kaddamar Da Yaki Akanta

kakakin harkokin wajen iran yace amurka ce ta fara kai mata hari amma tana so duniya ta biya farashi

Isma’il baqa’I kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ya sanar a shafinsa na X da yake bayani game da dalilan da suka jawo rashin tsaro a mashigar Hurmuz da kuma kawo cikas ga zirga-zirgan jiragen ruwa na kasuwanci na kasa da kasa, ya ce mashigar hurzmu a bude take tun ranar 28 ga watan fabareru  lokacin da kasar Amurka da Isra’ila suka kaddamar da yaki kan kasar Iran

Baqa’I ya kara da cewa Washington ta dorawa yankin yakin da ya sabama doka kuma ya jawo cikas ga zirga-zirgan jiragen ruwa a yankin ,safarar man fetur ya tsaya cak, kasuwancin ya tsaya, kuma ya jawo farashin makamashi yayi tashin goron zabi

kakakin ma’aikatar harkokin wajen na iran yace yanzu Amurka tana ta yada karerayin cewa iran ce ta jawo rashin tsaro da zaman lafiya a yankin, wanda ita kanta Amurkan ta san itace ummul habaisi, amma tana so ta tilasatawa dukkan duniya ta biya farashin matakin da ta dauka da ya sabama dokokin kasa da kasa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted