Abdullahiyan: Ba Zamu Mika Kaiba Ga Makiya Ba

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa kimani shekaru 70 dasuka gabata, bata taba jin wata kasa ta mayar mata da martani a

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa kimani shekaru 70 dasuka gabata, bata taba jin wata kasa ta mayar mata da martani a wani yaki ba, sai kasar Iran. Tana tsammanin kamar sauran kasashe Iran zata mika kai

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Janar Ali Abdullahi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran kuma shugaban cibiyar tsaro ta Khatamul Anbiya (s) yana fadar haka a wata hira ta musamman da aka yi da shi dangane da yakin kayakin lantarko ko “cyber war” da ke gudana a halin yanzu tsakanin Iran da makiyanta.

Yace yakin kayakin kumfuta yaki ne wanda aka dade ana fafatawa da makiya, da yardar All..a wannan karon ma ba zasu tsiraba. Duk da cewa yakin na yanzu ya zo ne bayan sun kasa kaiwa da manufofinsu a yakin da makamai na wuta.

Abdullahi ya kammala da cewa al-umma wacce ta dogara da All.. a ko yauce itace mai samun nasara. Ya ce, Amurka ba zata taba kaiwa ga manufofinta a wannan yakin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted