Kungiyoyin Agaji na kasar Lebanon sun ambaci cewa an sami shahidai da ba su gaza 10 ba, yayin da wasu 7 su ka jikkata saboda harin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai w agarin Kafar-Ruman akudancin Lebanon.
Kamfanin dillancin labarun kasar Lebanon ya sanar da cewa; Isra’ila ta tafka wani kisan kiyashi a garin kafar Ruman, da mutane 9 su ka yi shahada sai kuma wasu mutane 5 da su ka jikkata.”
Labarin ya ce; sojojin haramtacciyar kasar Isra’ilan sun kai hari ne da tsakar daren jiya akan wani gida mai hawa uku, da hakan ya yi sanadiyyar rushewar gidan baki daya.
Haka nan kuma labarin ya ce;Ma’aikatan agaji sun nufi wurin da aka kai wa harin inda su ka fito da gawawwakin shahidai9 daga cikinsu har da jarirai guda biyu, da kuma wadanda su ka jikkata su 5.
Har ila yau hare-haren sojojin na Haramtacciyar Kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar shahadar ma’aikata agaji 2 na kungiyar “Ar-Rilasah” da su ne Ali Shahrur da kuma Hadi Farhat.
Shugaban kasar ta Lebanon Joseph Aun ya bayyana harin da cewa yana da hatsari tare da yin kira ga Amurka da ta dakatar da Isra’ila.
Hare-haren na Haramtacciyar Kasar Isra’ila ci gaba ne da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ta kulla da Lebanon. Wannan kuma ba shi ne karon farko da ‘yan sahayoniyar suke keta yarjejeniyar ba.