Akalla Falasdinawa 5 Ne Suka yi Shahada Ciki Har Da Yara 2

falasdinawa 5 ne suka yi shahada a hare haren da isra'il ta kai a yankin

A hare haren da gwamnatin isra’ila ta kaddamar a yankin Gaza da safiyar yau litinin a yankin gaza akalla mutane biyar ne suka yi shahada ciki har da wasu yara kanana guda 2, kuma sun kai hari a yankunan Dairul balah da khan yunus, kuma sun samu wasu falasdinawa a yammacin gaza

Haka zalika wani yaro yayi shahada wasu kuma da dama sun jikkata a wani hari da sojojin isra’ila suka kai a wata makaranta a gabshin deir balah tsakiyar gaza, kamar yadda wasu kuma suka jikkata bayan da jirgin yakin Isra’ila ya kai harin kan wani gungun mutane a kusa da wajen cin abincin na dabun dake yammacin gaza

Wani bafalasdine yayi shahada bayan yayi fama da rauni da yaji sakamakon harbinsa da sojojin isra’ila suka yi a kusa da filin wasan na falasdin dake yammacin gaza

wannan yana zuwa ne a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma da isra’ila, inda sojojin ta suke kai hare hare da jiragen yaki da makami mai linzami kan gidajen mutane da kan ababen more rayuwa da kuma kashe falasdinawa hakan siddan

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted