Rundunar ruwa ko Navy ta dakarun kare juyin juya halin musulunci IRGC sun wargaza wani jirgin ruwa na yaki marasa matuki wanda yake kokarin shiga yankin mashigar ruwa ta Hurmuz.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto majiyar ta IRGC na cewa, bayan da sojojin Amurka suka kasa shigowa mashigar ruwa ta Hurmuz da manya manyan jiragen ruwa sun fara amfani da kananan jiragen ruwa, wadanda ake sarrafasu daga nesa.
Wannan jirgin ya yi kokarin shiga yankin da gwamnatin JMI ta kebe a mashigar don aikin leken asiri ko kuma kai hare hare, amma dakarun Navy suka ganoshi suka kuma wargaza shi a yau Lahadi.
Daga karshe bayanin ya bayyana cewa, dole ne sojojin Amurka su fice daga yankin yammacin Asia, idan suna son zaman lafiya.