Farashin Man Fetur Ya Kama Hanyar Dala 120 A Kowace Ganga Daya

Bankin " Goldman Sachs " na Amurka mai hada-hadar kula da harkokin kudi da kasuwanci ya yi gargadin cewa; Idan aka ci gaba da kai
hauhawar farashi

Bankin ” Goldman Sachs ” na Amurka mai hada-hadar  kula da harkokin kudi da kasuwanci ya yi gargadin cewa; Idan aka ci gaba da kai wa jiragen dakon man fetur hare-hare, to kuwa farashin man fetur zai iya kai wa Dala 120 kowace ganga daya.

Jami’i a wannan  Bankin wanda yake kula da Nazari akan farashin haja a kasuwannin duniya, Dan Sitrophen ya ce; Abubuwan da suke faruwa a cikin kwanaki kadan nan da su ka gaba, suna a matsayin gargadi ne akan yiyuwar fadadar hatsari ga yankunan da ake jigilar jiragen ruwa.

Farashin kowace gangar man fetur samfurin “Brent’ ya karu zuwa Dala 97 da shi ne mafi tsada tun daga watan Yuli.  Karuwar farashin dai ya biyo ne bayan hare-haren da aka kai akan jiragen ruwa a yankin tekun Pasha.

Sai dai kuma Bankin ya ce idan ma an sami raguwar tashe-tashen hankula a yankin tekun pasha, to farashin ba zai yi kasa da Dala 80 ba.

A daya gefen, jami’in Dan Sitrophen ya yi kira da yi dari-dari wajen zuba hannun jari na lokaci mai tsawo a cikin fagagen kasuwannin Gas na duniya da kuma dangogin man fetur.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted