Sakataren majalisar koli ta staron kasar Iran janaral muhsin rida’I a cikin wani bayani da yayi ta gidan talabijin din kasa ya nuna cewa mashigar Hurmuz a rufe take baki daya, yan mai kore bayanan da shugaban Amurka Donald trump yayi kan mashigar cewa abude take a matsayi karye ce kawai ya shirga.
Haka zalika ya bayyana cewa kafin rufe mashigar ya kasance akalla jirgen ruwa 100 ne dauke da kayyakin da suka kai nauyin miliyoyin tan,suke wuce wa, sai dai yanzu jiragen da suke wucewa ta wajen basu wuce guda 7 ba da suke dauke da muhimman kayayyakin bukata na alummar iran
Janar rida’I ya kara da cewa nan da yan kwanaki masu zuwa za’a sanar da yankunan da aka killace a wajen mashigar Hurmuz, wanda zai fara daga inda jiragen ruwa Amurka suke har zuwa cikin yankuna a tekun fasha, kuma iran za ta sanya takunkumi kan duk jirgin ruwa da ya shiga wannan yankin
Daga karshe janar Rida’I yace cikin saoi 48 da suka gabata an yi gwajin makamai masu linzami na kasar iran a karon farko a saman daya daga cikin jiragen yakin Amurka dake wajen, ya jaddada cewa wannan makamin mai linzami ya zama tamkar jahannama ce aka bude ga Amurka wannan yasa suka tsere daga wajen