Sojin Yamen Sun Sanar Da Kakkabo Jirgin Leken Asirin Saudiya

dakarun sojin kasar yamen sun kakkabo jirgin leken asirin kasar saudiya

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin kasar Yamen sun sanar da harbo wani  jirgin saman leken asiri na kasar  saudiya da safiyar yau litinin a sararin samaniya yankin  Khabb wa da sha’af dake lardin jauf

A cikin bayanan da yayi kakakin sojin kasar yamen yahya Saree yace jirgin leken asirin samfarin CH4 ne kuma an kakkabo shi ne adaidai lokacin da yake keta hurumin sararin samaniyar kasar a garin khub wa da sha’ab wannan yasa aka yi amfani da makamin da ya dace wajen harbo shi,

Haka zalika rahotanni da gidan talabijin din almayadeen ya nakato daga hedkwatar sojin kasar yamen ya nuna hare haren da dakarun sojin kasar yamen suke kai ya mayar da hankali ne kan shuwagabanin kungiyoyin sa kai na saudiya kuma yayi ishara da cewa suna samun nasara kan hare haren da suke kai wa.

 Dakarun na yamen sun jaddada cewa zasu mayar da martani mai tsanani kan duk wani hari da aka kawo musu, yace idan kasar saudiya ta yanke shawarar kaddamar da yaki akanta to dakarun sojin yamen za su mayar da martanin da ya dace mai tsanani a bangarori daban daban

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted