Yemen Ta Kai Hare Hare Kan Rumbun Makamai A Sharurah

Sojojin kasar Yemen sun bada labarin kai hare hare masu karfi a kan rumbun ajiyar makamai na kasar Saudia a garin Sharurah ta kudu. Tashar

Sojojin kasar Yemen sun bada labarin kai hare hare masu karfi a kan rumbun ajiyar makamai na kasar Saudia a garin Sharurah ta kudu.

Tashar talabijan ta AL-Masira ta nakalto kakakin sojojin kasar Burgedia Yahyah Saree yana fadar haka a jiya Asabar.

Ya kuma kara da cewa  sun yi amfani da makamai masu linzami da kuma makaman Drones a hare haren. Ya kuma kara da cewa, sun kai hare haren ne saboda maida martanai ga sojojin kasar Saudia wadanda suka bude wasu fagagen fama da sojojin kasar ta Yemen.

Majiyar gwamnatin Yemen ta bayyana cewa kokarin da kasar saudia take na bude sabbin fagagen fama ba zai wuce ba tare da maida martani ba. Tace duk wasu sabbin hare hare ba zasu wuce ba tare da sojojin yemen sun maida martani masu tsanani ba.

A wani labarin kuma gwamnatin kasar Saudia ta tabbatar da aukuwar hare haredaga kasar Yemen a lardin Sharurah ba tare da karin bayani ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted