Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran sharia ta kasa da kasa Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa jawabin bayan taro na kungiyar kasashen BRICS karo na 18 ya amince da manya manyan manufofin JMI kan al-amura da dama na kasa da kasa.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Gharibabadi yana fadar haka a jiya Asabarya kuma kara da cewa matsayin JMI dangane da al-amura wadanda suka shafi shirinta na makamashin Nukliya, harkokin kasuwanci ta duniya, Falasdinu da kuma matsalolin tsaro a halin yanzu a yammacin Asia duk sun yi dai dai da manya manyan manufofin JIM wanda kungiyar BRIKC ta tabbatar da su.
Ghariba Abadi ya bayyana cewa sashe na 29 na bayanin ya bayyana damuwar kungiyar kan yanda ba tare da wata tsokana ba, a dai dai lokacinda hukumar IAEA take kula da cibiyar makamashin nukliya na wata kasa, za’a kaiwa wannan cibiyar hare hare kamar yanda Amurka da HKI suka aikata a shekara da 2025 a kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran a fordo Natanz da Esfahan.
Sashe na 20 ya bukaci a bar Iran ta shiga hukumar kasuwanci ta duniya WTO da kuma sauran kasashen duniya wadanda suka cika sharuddan yin haka ba tare da tsongwama ba.
A bangaren hukumoni da cibiyoyin duniya, Kungiuyar BRICS ta bukaci a gudanar da sauye sauyen a MDD musamman a kwamitin tsaro, hukumar Lamuni ta duniya IMF, ta yanda zasu tafi dai dai da bukatun wasu kasashe a Africa, Asia da Laten Amerika.
Dangane da Falasdinu da Lebanon kuma kungiyar BRIKCS ta bayyana damuwarta yanda take hakkin bil’adama yake aukuwa a Palasdinu musamman gaza da Siriya kuma Lebanon.