A karshen taron na “Brics” an fitar da bayani wanda ya bayyana matsayar kungiyar akan batutuwa da dama a fagen siyasar duniya.
Bayanin kungiyar ya nuna kin amincewa da kakaba takunkumi ta gefe daya wanda yake cin karo da dokokin kasa da kasa. Haka nan kuma bayanin ya yi kira da a kira tafiyar da al’amurran duniya ta hanyar amfani ra’ayoyin bangarori mabanbanta wanda kuma zai zama mai girmama juna.
A cikin bayanin bayan taron na kungiyar “Bricks” an kuma yi kira ga kare hadin kan kasar Syria da dunkulewarta wuri guda.
Akan Lebanon kuwa, kungiyar ta yi kira ga sojojin mamayar Isra’ila da su fice daga inda su ka mamaye da kawo karshen keta hurumin kasar da suke yi.
An kafa kungiyar “Bricks” ne a 2009 domin karfafa tattalin arzikin kasashen masu tasowa da su ka hada Brazil, Rasha, India, da China. Daga baya kasar Afirka ta kudu ta shiga cikin wannan sabuwar kungiya da zummar samar da daidaito a fagen siyasar kasa da kasa.
Wasu kasashen da su ka zama mambobi daga baya, sun hada Iran, Saudiyya da UAE.
Ganawar Shugaban Kasar Iran Da Yarima Mai Jiran Gado Na UAE A India
A bayan taron kungiyar “Brics” a kasar Indiya, an yi ganawa a tsakanin shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkiyan da Yarima mai jiran gado na UAE Khalid Bin Muhamad Bin Zayid al-Nahyan.
Shugaban kasar ta Iran Dr. Pezeshkiyan ya je kasar Indiya ne domin halartar taron kungiyar “Brics” na kwana biyu domin tattauna hanyoyin bunkasa tattalin arziki.
Shugaban kasar na Iran ya gana da shugabannin kasashe daban-daban da su ka hada da mai masaukin baki na Indiya Droupadi Murmu da Fira ministanta Narendra Modi.