Shugaban kasar Iran Dr Masoud Peazeshkiyan ya ce ba za’a sami zaman lafiya a ko ina ba matukar wasu kasashe suna bari a yi amfani da kasashensu don kaiwa wata kasa hare hare.
Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a lokacinda yake jawabi na karshe a taron shuwagabannin kungiyar BRIKCS karo na 18 wanda aka kammala a birnin New Delhi na kasar Indioya. A jiya Asabar.
Ya ce ya haka babban laifi ne kamar yanda ya zo a dokokin kasa da kasa da dama. Amma abin bakinciki a farkon wannan shekarar Amurka da HKI sun yi amfani da wasu kasashe makobta Ira n don kaimata hara hare. Wanda kuma ya kaiga halin tarbarewar harkokin tsaro a yankin.