Afirka Ta Kudu Za Ta Mika ‘Yan Nigeria 6 Ga Amurka Saboda Zambar Dala Miliyan 6 Ta Hanyar Internet

'Yan Nigeria 6 Da Aka Kama A Afirka Ta Kudu Za Su Fuskanci Shari'a A Amurka Saboda Zambar Dala Miliyan 6 Ta Hanyar Internet
shugaba Remaphosa

‘yan sanda kasar Afirka Ta Kudu sun ce za su mika wa Amurka wasu ‘yan asalin kasar Nigeria su 6 saboda alakarsu da damfarar Dala miliyan 6 da su ka yi wa wasu matan Amurka ta hanar internet da sunan soyayya.

Mutanen dai an kama su ne tun a 2021 a garin “Cape”, kuma za a mika su ga hukumar bincike ta ‘yan sandan Amurka ( FBI). Laifin da ake tuhumarsu da shi, yana karkashin damfara da kuma wanke kudin haram.

“Yan sandan Afirka Ta Kudu sun ce, mutane sun yi mu’amala da mata fiye da 100 ‘yan Amurka, da su ka iya matsarsu dala Miliyan 6 da sunan soyayya ta bogi ta Internet.

‘Yan sanda na kasa da kasa ” Interpol” ne su ka shiga Tsakani domin mika ‘yan Nigeria din da za dauke su zuwa kasar Amurka.”

Kakakin ‘yan sandan Afirka ta Kudu Katlego Mogale ya ce; hukumar ‘yan sanda masu bincike ta Amurka FBI tuni sun isa kasar domin karbar ‘yan Nigeria da tafiya da su zuwa can kasar Amurka.

Binciken da hkumar ‘yan sanda ta kasa da kasa take yi a yammacin Afirka dangane da masu aikata tsararrun laifuka ya yi sanadiyyar kama mutane 58 da kuma gano wasu 263 masu alaka da laifuka irin wadannan.

A kasar Afirka Ta Kudu kadai, jami’an ‘yan sanda sun kai farmaki a wurare mabanbanta da su ka hada da birnin Johannesburgh tare da kame mai laifuka damfara na kasa da kasa ta kafar sadarwa ta Inernet. Haka nan kuma sun yi nasarar kwace kudaden da sun kai Dala miliyan 2.67 da kuma rufe asusu-asusu a Bankuna har guda 250.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted