Iraki Ta Musanta Kai Hari Kan Bututun Man Saudiya

Dakarun musulunci masu gwagwarmaya a kasar Iraki wato Hashashaabi sun barranta kansu daga kai hare hare a kan bututan man fetur na kasar Saudia. Sun

Dakarun musulunci masu gwagwarmaya a kasar Iraki wato Hashashaabi sun barranta kansu daga kai hare hare a kan bututan man fetur na kasar Saudia. Sun kuma bayyana goyon bayansu ga mutanen kasar yemen wadanda suke fafatawa da mayakan kasar saudia a halin yansuzu.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar hashdu shaabi na cewa, zargin da akewa yayan kungiyar da kai hare hare a kan kayakin man fetur a kasar saudia ba gaskiya bane. Kuma dakarun ba zasu sa kansu a cikin rigima da kasar saudia don hakan zai faranta ran makiya ne kawai.

Dakarun sun yi kira ga gwamnatin kasar Iraki kada ta yi saurin amincewa da kuma yanke hukunci dangane da wannan zargin. Banda haka hashdu shaabi ta kara da cewa a shirye take ta bayyana a gaban duk wani kwamitin bincike wanda zata kafa don gano gaskiyar abinda ya faru.

Dakarun sun kara da cewa suna goyon bayan kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen kan fafatawar da take yi da kasar Saudia don kawo karshen killacewar da ta yi wa kasar Fiye da shekaru 10 da suka gabata..

Gwamnatin kasar Iraqi dai ta rufe mashigar kan iyakokin kasashen Iraki da Iran guda biyu saboda abinda ta kira saboda magance matsalolin tsaro na wani karamin lokaci, amma masana suna ganin rufewar ba zai rasa nassaba lalata bututun man na kasar saudia ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted